• Labaran yau

  Takaddama kan waye zai ciyar da Dino Melaye a asibiti, yansanda sun ja daga

  Wata tawaga daga Majalisar Dattawa ta Najeriya karkashin jagorancin Sanata Bala Ibn Na'Allah tare da wasu Sanatoci sun kai ziyara a Asibitin tarayya wajen da yansanda ke ci gaba da sintiri yayin da Sanata Dino Melaye yake jinya a Abuja.

  An sami takaddama dangane da yadda za'a ciyar da Melaye,Asibiti ko yansanda, haka zalika daga karshe an yi itifaki a kan cewa za a samo wanda zai ciyar da shi daga waje amma dole sai ya dandana abincin kafin a ba Melaye.

  Majiyarmu ta shaida mana cewa yansanda sun so su tafi da Dino Melaye wanda ke kwance a dakin da ake kula da masu ciwon da ya yi tsanani ICU cewa idan har ya zama dole yansanda su dauki Melaye to wajibi ne yansanda su rubuta haka zuwa ga hukumar Asibitin.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Takaddama kan waye zai ciyar da Dino Melaye a asibiti, yansanda sun ja daga Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama