• Labaran yau

  Sojin briged na 47 sun gina sabon wajen tsare yan ta'adda a Maiduguri - Hotuna

  Rundunar sojin Najeriya ta gina wani cibiya na zamani domin tsare yan ta'adda a Barikin Giwa da ke Maiduguri. Injiniyoyin soji na Birged na 47 suka gina cibiyar wanda ke da sashe biyu.

  Kowane sashe yana da tsari na zukar zafi da doyi tare da ban daki da rijiyoyin burtsatse da za su samar da wadataccen ruwa a ko da yaushe.

  Babban kwamanda mai kula da yaki da boko haram na Operation Lafiya Dole Manjo Janar Rogers Nicholas ne ya kaddamar da cibiyar ranar Asabar.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sojin briged na 47 sun gina sabon wajen tsare yan ta'adda a Maiduguri - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama