• Labaran yau

  Saurayi ya yi wa budurwa duka domin ta ki ta aminta da shi

  Wani matashi dan shekara 30 ya fada hannun hukumomi bayan ya yi wa budurwarsa dan karen duka domin ta ki ta aminta da shi,sakamakon haka Kabiru Tajuddeen ya huce haushin sa a kan ta ta hanyar duka.Lamarin ya faru ne a unguwar Omoroga kusa da bututun Meiran a karamar hukumar Alimosho da ke jihar Lagos.

  Yarinyar mai suna Omowumi Omoroga ta ba Tajuddeen mamaki bayan ta ki ta aminta da shi a lokacin da ya nemi ya biya bukatarsa, ita kuma ta dage tare da turjewa a kan cewa ita fa ba irin wadadnnan matan bace. Lamarin ya ba tajuddeen kunya da takaici.

  Bayan haka ne washe gari suka sami matsala da Tajuddeen wanda ya yi amfani da wannan dama ya yi ma Omowomi dukar tsiya har da raauni a fuska. Daga bisani an kai ta Asibiti kuma an yi mata magani.

  Wannan lamari ya kai har ofishin yansanda a Meiran wanda suka kama Tjuddeen suka kulle shi kuma suka bincike shi, daga bisani suka gurfanar da shi a gaban Kotun Ogba bisa zargin duka da raunata Omowumi amma bai amsa laifinsa ba.

  Daga bisani Alkalin Kotun Mrs. Jadesola Adeyemi-Ajayi ta bayar da belin Tajuddeen akan N50.000, an dage shari'ar zuwa ranar 7 ga watan Mayu 2018.Daga bsani an tasa keyarsa zuwa Kurkuku kafin ya cika ka'idar beli.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Saurayi ya yi wa budurwa duka domin ta ki ta aminta da shi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama