• Labaran yau

  Rikicin kabilanci ya yi sanadin mutuwar mutum 20 a jihar Nassarawa - Hotuna

  Wani rahotu daga jihar Nassarawa ya nuna cewa an sami tashin hankali ranar Talata wanda yake da nassaba da kabilanci tsakanin  al'ummar Ebira da Bassa da basu ga maciji da juna a kauyen Ugya da ke karamar hukumar Toto a jihar Nassaarawa. Fiye da mutum 20 ne ake faragaban sun mutu sakamakon rikicin yayin da da dama suka sami raunuka.

  Rahoton ya kara da cewa kimanin yan babura 30 ne dauke da mutum 3 kowanensu suka kai hari a kauyen wanda daga bisani suka yi arangama da sojoji sakamakon haka sojoji suka rinjaye su.

  An kama da yawa daga cikin wadanda suka yi aika-aikan kuma suna hannun soji yayin da ake ci gaba da bincike.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rikicin kabilanci ya yi sanadin mutuwar mutum 20 a jihar Nassarawa - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama