• Labaran yau

  Majalisar Dattawa ta gayyaci safeto janar na yansanda kan Dino Melaye

  Majalisar Dattawa ta Najeriya ta nuna rashin jin dadinta sakamakon yadda yansanda suka kama Sanata Dino Melaye da kuma wulakanci da ya fuskanta sakamakon haka.

  Bayan an bi ka'idodin zaman Majalisar, daga bisani Majalisar  ta aminta da a gayyato Babban safeto janar na yansandan Najeriya domin ya yi ma Majalisar karin bayani a kan halin da Melaye yake ciki ranar Alhamis.

  Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya tura wata tawagan Sanatoci domin su  bincika halin da Dino Melaye yake ciki a babban Asibitin tarayya da ke Abuja.


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Majalisar Dattawa ta gayyaci safeto janar na yansanda kan Dino Melaye Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama