• Labaran yau

  Mabiya Shi'a sun sake yin arangama da yansanda a Abuja

  Rahotanni da suka fito daga kafafen watsa labari a Najeriya sun nuna cewa an sake yin arangama tsakanin yan Shi'a da 'yansanda a babban birnin tarayya Abuja.

  RFI ta labarta cewa an kara samun arangama tsakanin mabiya Shi’a da jami’an ‘Yansanda a Abuja babban birnin Najeriya, bayan wata zanga-zanga da suka kara gudanarwa yau don neman sakin jagoransu Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky.
  Wanann dai shi ne karo na biyu da mabiya Shi’an suka gudanar da zanga-zanga cikin kasa da kwana goma inda a ranar 16 ga watan Aprilu jami’an ‘yansanda suka kame akalla mabiyan 15 bayan zanga-zangar da ta kai ga barnata kadadrorin jama’a da na gwamnati.

  Jami'an tsaron sun yi amfani da karfin tuwo don tarwatsa masu zanga-zangar kamar yadda ya faru a makon jiya inda aka yi amfani da hayaki mai sanya hawaye don tarwatsa su.

  Hukumomin kare hakkin dan adam dai na ganin gwamnatin Najeriyar ta ki mutunta umarnin da aka bata na sakin Sheikh Ibrahim Zakzaky, ko da ya ke dai tana ikirarin cewa tana kare lafiyarsa ne la'akari da cewa rayuwarsa na cikin hadari
  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mabiya Shi'a sun sake yin arangama da yansanda a Abuja Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama