• Labaran yau

  Kwacewar burki ya sa motar tipa ta markade yansanda 2 a jihar Delta

  Wasu jami'an yansanda guda biyu sun gamu da ajalinsu bayan wata motar tipa ta bi ta kansu sakamakon kwacewar burki.Nan take jami'an suka mutu bayan motar ta takesu a gadar Headon da ke garin Asaba na jihar Delta.

  Rahotanni sun ce yansandan na aikin sintiri ne a kan hanya, kwatsam sai burki ya gaza sakamakon haka motar ta kwace ta taho a guje ta bi ta kan yansandan su biyu.

  Fasinjoji da ke wucewa ne suka jaye gawakin yansandan daga kan hanyar mota.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kwacewar burki ya sa motar tipa ta markade yansanda 2 a jihar Delta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama