• Labaran yau

  Ku yi shirin yakin ganin an kifar da shugaba Buhari a zaben 2019 - Obasanjo

  Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bukaci 'yayan kungiyar Coalition for Nigerian Movement CNM su yi shirin yakin ganin cewa sun karbe mulki daga hannun shuga Buhari a 2019.

  Obasanjo ya yi wannan jawabi ne a lokaci kaddamar da reshen kungiyar na jihar Oyo a Trans Amusement Park ranar Asabar.

  Ya kara da cewa "Buhari ya kasa sakamakon haka zai zama babban kuskure a sake abensa a 2019.

  Za su yi kokarin yi maku barazana, amma ku yi kokari ku sami PVC a hannu kuma ku yarda cewa Allah zai yi abin al'ajabi a 2019 kamar yadda ya yi a baya. Ba na shakkar komi domin dai har Kurkuku aka kai ni a kan abin da ban ji kuma ban gani ba".

  Obasanjo ya ci gaba da cewa "A matsayi na na wanda ya kirkiro wannan akidar, babu yadda za a yi in kyale ku, za ku same ni a duk lokacin da hakan ya taso kuma an bayar da nawa gudunmawa.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ku yi shirin yakin ganin an kifar da shugaba Buhari a zaben 2019 - Obasanjo Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama