• Labaran yau


  Kotu ta saki yan boko haram 2 sakamakon rashin gabatar da shaidu

  Wata babban Kotun tarayya a Abuja ta saki wasu mutum biyu da aka gurfanar a gabanta bisa zargin kasancewa yan kungiyar boko haram shekara biyar da suka wuce.Wadanda aka saki sune Ibrahim Ahmed da Sani Argungu.

  Mai shari'a Justice Binta Nyako ta ce Kotu ta saki wadanda ake tuhuma ne sakamakon gazawar masu shigar da kara na gwamnatin tarayya su gabatar mata da shaidu a kan mutanen ganin cewa wadanda ake tuhuma suna tsare tun 2012.

  Justice Nyako ta bukaci wadanda aka sake kada su yi cudani da bata gari kuma za'a sa ido akan harkokin su. Haka zalika ta ce a duk lokacin da masu gabatar da kara suka gama hada shaidu za su iya sake gabatar da su domin a ci gaba da shari'ar.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta saki yan boko haram 2 sakamakon rashin gabatar da shaidu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama