• Labaran yau

  Ko su waye suka kashe wani mutum a gidansa a Gusau jihar Zamfara ?

  Ibtila'in yawan kashe kashen bayin Allah ya zama ruwan dare a jihar Zamfara. a garin Gusau babban birnin jihar ta Zamfara wasu da ake zargin cewa yan daba ne sun shiga gidan wani bawan Allah suka yi masa kisar gilla ta hanyar sassare shi lamari da ya sa ya mutu nan take.

  Hukumomi a jihar ta Zamfara sun dauki sabbin matakai da ya shafi tsari na hadin guiwa tsakanin dakarun musamman na sojin sama, sojin kasa tare da jami'an yansanda domin ganin cewa an inganta harkar tsaro a jihar ta Zamfara.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ko su waye suka kashe wani mutum a gidansa a Gusau jihar Zamfara ? Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama