• Labaran yau

  Karanta dalilin da ya sa wannan mutum ya yi wa yar shekara 12 fyade

  Hukumar yansanda a jihar Niger ta kama wani mutum dan shekara 25 bayan ya taushe wata yarinya yar shekara 12 ya yi mata fyade a cikin wani kangon gida a garin Madalla a karamar hukumar Suleja da ke cikin jihar Niger.

  Kakakin hukumar yansanda na jihar Niger Muhammed Abubakar ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ya kara da cewa ce baya jin dadin tarayya da manyan mata sai yan yara kanana.

  Haka zalika ya ce hukumar yansanda ta kammala bincike a kan lamarin kuma za ta gurfanar da shi a gaban Kotu.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karanta dalilin da ya sa wannan mutum ya yi wa yar shekara 12 fyade Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama