• Labaran yau

  Karanta abin da ya faru bayan direbobin bas sun fara yajin aiki a Afrika ta kudu

  Rahotanni daga kasar Afrika ta kudu sun nuna cewa yanzu haka an fara gudanar da yajin aiki da direbobin motocin bas suka kuduri aniyar yi.

  TRT ta labarta cewa dubunnan al’umar Afirka ta Kudu sun shiga hali ni ‘yasu sakamakon yajin aiki da direbobin motocin bas suka fara a fadin kasar wadanda suke neman a kara kyautata yanayin aikinsu.

  Tun ranar Litinin din da ta gabata aka fara yajin aikin wanda aka ekuma ci gaba bayan da direbobin suka kasa cimma matsaya da hukumomi.

  Kakakin Kungiyar Matuka Motocin haya ta Afirka ta Kudu Zanele Sabela ta bayyana cewa, direbobin na neman karin albashin kaso 9.5 cikin dari amma kuma masu motocin sun ki amince wa da hakan.

  Matukin motar bas a Afirka ta Kudu na samun dala 500 a wata inda a kowacce rana ya ke aikin kusan awanni 10.
  Yajin aikin ma’aikata abu ne ruwan dare a Afirka ta Kudu.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karanta abin da ya faru bayan direbobin bas sun fara yajin aiki a Afrika ta kudu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama