• Labaran yau

  Karanta abin da aka yi kafin a binne wannan gawar - Hotuna

  Bikin bizine gawar wani tsoho a Port Harcourt na jihar Rivers ya jawo hankalin jama duk da yake irin wannan abu ba wani abin mamaki bane a wannan yankin.An bizine John Chituru Amadi bayan an gudanar da ka'idodi na gargajiya da ya hada da sare kan wani kare da wata akuya.

  Babban dan mamacin ne ya sare kawunan wadannan dabbobi.

  Bayanai sun ce a bisa al'adar wannan al'umma, dole ne babban dan mamacin ya yi amfani da adda ya kai sara daya tak wanda zai sare kan kare da akuyar kowanen su. An ce idan an sami akasi yaron ya kai sara amma sai kan kare ko na akuya bai fille ba tau lamarin ya gamu da la'ana na kakanni kenan.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karanta abin da aka yi kafin a binne wannan gawar - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama