• Labaran yau

  Ka san ko wacece "first lady" a tsakanin matan gwamnan jihar Kebbi ?

  Wani bayani da ya fito daga shafin sada zumuntan Twitter na gwamnatin jihar Kebbi ya bukaci jaridar dailytrust ta yi gyara a wani labari da ta wallafa inda ta ambato Aisha Atiku Bagudu a matsayin "first lady" kuma ta bukaci a gyara zuwa Zainab Atiku Bagudu ce "first lady".Dukannin matan biyu matan Gwamnan jihar Kebbi ne Sanata Abubakat Atiku Bagudu.

  To amma bayanai sun nuna cewa Aisha ce aka fara aurowa kafin Zainab, wanda ke nuna a al'adance Aisha ce yaya kenan .

  Tuni dai wannan lamari ya jawo kace-nace a shafukan sada zumunta musamman zauruka da ke da alaka da jihar Kebbi.

  Sai dai wani jin ra'ayin jama'a da ISYAKU.COM ya gudanar ya nuna cewa kashi 80 na wadanda muka zanta da su sun nuna cewa a bar wannan lamarin ga maigida watau Gwamna Bagudu ya warware shi da kanshi kuma ba daidai ne a yi masa katsalandan a al'amarin gidansa ba.

  A gefe daya kuma wasu jama'a sun nuna cewa lamarin na jihar Kebbi ne domin yanzu Gwamna Bagudu jama'ar jihar Kebbi yake yi wa aika ba gidansa ba, sakamakon haka suna ganin adalci ya kamata a yi kuma a kawar da son rai.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ka san ko wacece "first lady" a tsakanin matan gwamnan jihar Kebbi ? Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama