• Labaran yau

  Ka san ko su waye suka fasa cikin wannan saurayi a Lagos ?

  Wani babban kalubale da ke fuskantar al'umma shi ne yawaitar harkar shaye-shaye a tsakanin matasa, wannan saurayi ya gamu da ajalinsa ne a hannun wasu matasa da ake kyautata zaton cewa yan shaye-shaye ne wanda suka burma cikinsa da wuka a unguwar Aboye da ke Ejigbo a jihar Lagos.

  PM News ta ruwaito cewa mazauna unguwar sun wayi gari ne suka gan gawar saurayin an burma cikinsa kuma sakamakon haka hanjin cikinsa suka fito yanayi da ya haifar da mutuwar saurayin.

  Majiyar mu ta ce lamarin ya faru ne a wani sashe na Ejigbo wurin da aka shaida cewa matattara ce ta masu aikata laifuka wuri kuma da mugan mutane ke yawan ziyarta .

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ka san ko su waye suka fasa cikin wannan saurayi a Lagos ? Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama