• Labaran yau

  Jam' iyar APC ta yi babban kamu, Ali Modu Sherif zai canja sheka zuwa APC

  Jam'iyar APC mai mulki a Najeriya ta bukaci Sanata Ali Modu Sheriff ya je mazabarsa a Ngala na jihar Borno domin ya yi rajistan kasancewa dan jam'iya.Sakataren watsa labarai na APC a Abuja Malam Bolaji Abdullahi ya ce jam'iyar ba ta karbar wadanda suka janja sheka a babban sakatariyar ta da ke Abuja.

  Sakamakon haka ya bukaci tsohon gwamnan na Borno ya je mazabarsa domin ya yi rijista.

  Abdullahi yana mayar da martani ne bisa wani labari a jaridu da ke nuna cewa tsohon gwamnan ya shirya tsaf domin ya canja sheka zuwa jam'iyar APC.

  Ali Modu Sheriff dai shi ne gwamnan Borno daga 2013 zuwa 2011.

  Ya kuma zama shugaban jam'iyar PDP na kasa na wucin gadi a 2016 a yanayi da ke cike da rudani da kalubale na shari'a wanda daga karshe bangaren Sanata Ahmed Makarfi da ke kalubalantar shi suka yi nassara a Kotu.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jam' iyar APC ta yi babban kamu, Ali Modu Sherif zai canja sheka zuwa APC Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama