• Labaran yau

  Direba ya kashe fasinja 12 bayan ya zagi jami'an FRSC a kan mugun gudu

  Wani mumunar hadarin mota ya auku a babban hanyar Lagos zuwa Ibadan bayan wata motar bas ta yi karo da wata babbar motar Volvo ta daukar kaya sakamakon mugun gudu lamari da ya yi sanadin mutuwar mutane 12 wadanda suka hada da maza 6 da mata 6.

  Majiyar mu ta labarta mana cewa tun farko jami'an FRSC da ke sintiri a hanyar sun gargadi direban da yake mugun gudu da motar bas mai lamba AAA 886 XR amma sai ya yi masu dakuwar zagi da hannunsa. Kasa da minti biyar kuwa sai ya yi kokarin wuce wata mota amma kaddara ta riga fata sai ya auka ma wata babbar mota kirar Ford mai lamba LSD 138XQ.

  Gabadaya mutum 20 ne hadarin ya rutsa da su maza 11 mata 9.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Direba ya kashe fasinja 12 bayan ya zagi jami'an FRSC a kan mugun gudu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama