• Labaran yau

  Dino Melaye ya ketare shirin kiraye sakamakon gazawar kuri'u

  Yunkurin kiraye ga Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma Dino Melaye ya ci tura sakamakon gazawar ci ma adadin yawan mutane da ake bukata kafin hakan ya tabbata.

  Kafin lamarin ya tabbata na kiraye, dole ne a sami kashi 50 da sa hannun mutum daya daga cikin wadanda suka rubuta takardar kirayen kafin ya yi nassara.

  Jami'in INEC da ke kula da aikin tantancewar Farfesa Ukertor Gabriel Moti, ya ce mutum 18,742 daga cikin mutum 189,870 ne aka tantance, Sakamakon haka ya ce kuri'un sun zama kashi 5.34 kenan daga cikin 351.146 a mazabar Sanatan.

  Daga karshe Farfesa Ukerto ya ce sakamakon gazawar ci ma ka'idar adadin da ake bukata, gaba daya shirin kiraye bai yi nassara ba.
   .
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dino Melaye ya ketare shirin kiraye sakamakon gazawar kuri'u Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama