• Labaran yau

  Dalilin da ya sa matar Sarkin Swaziland ta 8 ta kashe kanta

  Matar Sarki Mswati III na kasar Swaziland Senteni Masango wacce ita ce mata ta takwas 8 ga basaraken ta kashe kanta. Rahotanni sun ce ta kashe kanta ne ranar Juma'a wayewar Asabar.

  Wata majiya da ke kusa da mariganyar ta ce  Senteni Masango ta hadiye fiye da kapso 40 na amytriptyline wanda ake amfani da shi domin jinyar matsalar tabin hankali kuma majiyar ta ce ta yi haka ne sakamakon matsananci damuwa da take fuskanta a gidan Sarautar.

  Bayanai sun ce Sarkin ya hana ta ziyartar jana'izar kanwarta , haka zalika Basaraken bai ziyarce ta ba kusan shekara uku da aka tsare ta a wani katafaren Fada a gidan Sarki.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dalilin da ya sa matar Sarkin Swaziland ta 8 ta kashe kanta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama