• Labaran yau

  An yi wa sajen na yansanda koran kare daga aiki sakamakon kashe da acaba

  Hukumar yansada a jihar Ebonyi ta kori wani jami'in dansanda mai mukamin sajen mai suna  Onyebuchi Nweke bayan ya harbe wani dan acaba mai suna Ejika har lahira domin ya ki ya ba shi cin hanci na N50 a Abakaliki na jihar ta Ebonyi.

  Lamarin ya faru a kan hanyar Water works da ke Abakaliki ranar Laraba 25 ga watan Afrilu.

  Kakakin hukumar yansanda na jihar Loveth Odah ya ce an kama dansandan kuma an same shi da laifin aikata kisa da gangan a tsarin hukuncin yansanda na Orderly room, sakamakon haka aka yi masa koran kare daga aikin dansanda .

  Kakakin ya ce bayan haka hukumar za ta gurfanar da korarren dansandan a gaban Kotu bisa zargin kisan kai da gangan.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An yi wa sajen na yansanda koran kare daga aiki sakamakon kashe da acaba Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama