• Labaran yau

  An kashe Hausawa 11 tare da kone Masallatai 2 a sabon farmaki a Makurdi - Hotuna

  Akalla mutu 11 aka kashe yayin da aka raunata da dama bayan an kone wasu Masallatai biyu a wani hari da aka kai a kan al'umman Hausawa a garin Makurdi na jihar Benue.

  Mai ba gwamnan jihar Benue shawara kan harkokin addinin Musulunci Rilwanu Muhammed ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma yi harsashen cewa adadin zai iya zarce haka.

  Rilwanu ya ce akwai wasu karin mutum biyar wadanda ke kwance a Asibiti sakamakon raunuka da aka yi masu a lokacin  farmakin .

  Wannan ya faru ne bayan an kashe akalla mutum 16 ciki har da wasu Fada na Cocin Katolika guda biyu a jihar na Benue kwanaki biyu da suka gabata.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kashe Hausawa 11 tare da kone Masallatai 2 a sabon farmaki a Makurdi - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama