• Labaran yau

  An kama DCO da safeton yansanda bisa zargin kashe dan basarake a caji ofis

  Yan kwanakin da suka gabata ne labari ya bulla a shafukan yanar gizo cewa wani Yarima dan wani Basaraken gargajiya a jihar Ebonyi ya mutu a hannun yansanda yayin da yake tsare a hannunsu.Yanzu haka an sami karin haske a kan musabbabin wannan lamarin .

  Rahotanni daga Daily Crimes sun nuna cewa yansanda sun kama Yarima Kelechi Ineke dan Sarki Eze Gabriel Ineke a.k.a Echemugo na 1 na Al'ummar Abaomege a jihar Ebonyi bayan sun yi fada da dan wani safeton dansanda mai suna Umet Ekwe wanda ke aiki a ofishin yansanda a garin.

  Haka zalika rahoton ya yi zargin cewa bayan an kama Kelechi, an tsare shi, ya sha ukuba, aka hana shi abinci har kwana hudu daga bisani aka hana belinsa har tsawon wadannan kwanakin, daga karshe kuma ya mutu.

  Wani lamari mai daure kai cikin al'amarin shi ne yadda aka gan igiya daure a wuyar gawar Kelechi a lamari da ya yi kama da cewa ya kashe kanshi ne a cikin kurkukun ofishin yansanda.

  Daily Crimes ta ce wasu matasa da basu son a ambato sunayensu sun ce safeton ne da DCO na ofishin na yansanda su ne suka aikata wannan danyen aiki domin mahaifin yaron ya tsufa matuka kuma yana kwance a Asibiti.

  Bayanai sun ce DCO mai suna Eze Brendan Ikechukwu dan asalin Nsukka na jihar Enugu dama can akwai azazza tsakaninsa da Kelechi a kan wata budurwa wacce ta fi kaunar Kelechi a garin Abaomege, sakamakon haka lokacin da aka kama Kelechi aka kawo shi ofishin yansanda sai shi DCO ya yi amfani da wannan dama ya aikata abin da ransa ya nuna masa.

  Tuni dai Kwamishinan yansanda na jihar Ebonyi Mr, Titus Lamorde ya bayar da umarni a kama DCO da Safeto tare da dansa kuma aka maka masu ankwa aka tafi da su Abakaliki hedikwatar jihar Ebonyi domin gudanar da bincike a sashen CIID.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kama DCO da safeton yansanda bisa zargin kashe dan basarake a caji ofis Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });