• Labaran yau

  Yansanda sun bindige madugun kungiyar masu sace mutane don garkuwa


  Yansanda a jihar Edo sun bindige wani madugun wata kungiya wadda ke sace mutane domin karbar kudin fansa har lahira bayan kungiyarsa ta sace wani tsoho da ta yi garkuwa da shi a daren Talata.

  Jami'an yansanda sun yi nassarar ceto mutumin da aka yi garkuwa da shi bayan sun bindige jagorar kungiyar a wata musanyar wuta na harbi da bindigogi tsakanin yan kungiyar da yansanda a unguwar Falonu kusa da rukunin gidaje na Ekae GRA a birnin Benin na jihar Edo.


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yansanda sun bindige madugun kungiyar masu sace mutane don garkuwa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama