• Labaran yau

  Yadda wutar kendur ya yi sanadin mutuwar yara 3 'yan uwan juna

  Gobara ta halaka wasu yara 'yan uwan juna guda uku sakamakon wutar kendur da mahaifiyarsu ta kunna a cikin daki wanda daga bisani ya haddasa gobarar da ta yi sanadin mutuwar yaran a jihar Abia.

  Wadanda gobarar ta halaka su ne Chidera dan shekara 7, Destiny dan shekara 5 sai Precious 'yar shekara 3.

  Majiyarmu ta ce gobarar ta faru ne bayan mahaifiyar yaran watau Ugochi ta kunna kendur wanda aka aza a gefen kujera, daga bisani sai kendur ya fada a kan wata jaka da aka ajiye a gefen kujerar sai ta kama da wuta kuma mahaifiyar yaran ta kulle yaran a cikin dakin ta tafi wani gida domin ta sa cajin wayarta amma sai ta share da barci.

  Sakamakon haka dai yaran suka halaka a wutar gobarar.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda wutar kendur ya yi sanadin mutuwar yara 3 'yan uwan juna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama