• Labaran yau

  Yadda saurayi ya kashe kanshi sakamakon matsanancin damuwa

  Wani saurayi dan shekara 20 mai suna Umar Muhammed ya kashe kanshi bayan ya rataye kanshi a wata itaciya a kusa da wani rafi a unguwar Kandahar da ke cikin karamar hikumar Hadejia na jihar Jigawa.

  Rahotanni sun ce an gano gawar Umar ne tana lilo a wata itaciya a kusa da rafi, kafin jami'an tsaro su dauke gawar.

  Wata majiya ta ce saurayin yana fama da matsaanancin damuwa kafin lamarin ya faru.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda saurayi ya kashe kanshi sakamakon matsanancin damuwa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama