• Labaran yau

  Yadda aka kashe Buharin Daji tare da kwamandodinsa 6 - Hotuna

  Kusurgumin dan fashi, mai satan shanaye kuma uban yan ta'adda wanda Duniyar Zamfarawa, Katsinawa da Kaduna ke tsoro sakamakon irin yadda shi da yan kungiyarsa ke gudanar da ayyukan ta'addanci na rashin imani watau Buhari Tsoho wanda aka fi sani da suna Buharin daji ya gamu da ajalinsa bayan mataimakinsa ya bindige shi har lahira yan kwanakin da suka gabata.

  An haifi Buharin Daji a kauyen Dangulbi kusa da garin Dansadau a jihar Zamfara.Kafin mutuwarsa Buhari ya kasance mutumin da ke jagorantar daban ta'addancin da suka addabi jihohin Kaduna, Katsina da kuma mumunan kisan jama'a da aka yi a jihar Zamfara yan makonni da suka gabata.

  A yanayin tafiya da ta yi kama da ta kungiyar asiri na Mafia Buharin Daji ya gamu da cin amana kamar yadda shi ma ya dade yana aikatawa ga jama'a.

  Bayanai sun nuna cewa Buharin Daji ya kai wani hari a Ruggar Fulani a kauyen Katsinawa a jihar Zamfara inda ya sace shanaye mallakin surukin Gide Dogo wanda shi ne mataimakin Buharin Daji amma tun da dadewa ya canja sheka ya tuba kuma yana taimaka wa Gwamnati wajen tabbatar da kokarin ganin cewa an kawo karshen aikin ta'addanci na kashe kashe da satan shanu a jihar Zamfara.

  Sakamakon haka, Gide Dogo ya bukaci Buharin Daji ya sako wa surukinsa shanayensa amma sai ya ki har zuwa tsawon wani lokaci. Daga bisani Buharin Daji ya bukaci su hadu da Gide Dogo a wani kusurgumin daji da ke cike da tsaunuka a dajin Nabango a gundumar Goron Dutsi a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna domin su sasanta kansu.

  Ranar Laraba yayin da Buhari ya isa wajen da suka yi alkawarin cewa su hadu, isarsa ke da wuya sai Gide Dogo ya buda masa wuta da bindiga inda nan take ya kashe Buharin Daji tare da manyan kwamandodin sa masu kare lafiyarsa su shida wadanda suka mutu nan take. Daga bisani sai ya je ya gaya wa jami'an tsaro abin da ya aikata tare da kwatanta masu wajen da za su sami gawakin wadannan bata garin.

  Ko mutuwar Buharin Daji ya zama izna tare da kawo karshen fargaba da wannan yankin ke fama da shi kenan ? Lokaci ne kadai zai iya tabbatar da haka.

  Rahotu na Musamman daga Isyaku Garba.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda aka kashe Buharin Daji tare da kwamandodinsa 6 - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });