• Labaran yau

  Saurayi ya kashe budurwarsa domin ta ki ta zubar da cikin shege

  Wani saurayi dan aji 300 na Kwalejin koyon ayyukan shari'a na jihar Jigawa da ke Ringim mai suna Ringim Ismail ya kashe budurwarsa bayan ta ki ta aminta domin ta zubar da cikin shege da ya yi mata.

  Yansanda a jihar Jigawa suna tuhumar Isma'ila da kashe Salamatu Garba yar shekara 22 wacce ke unguwar rukunin gidajen Kofar Gabas da ke Jahun a jihar Jigawa ranar Asabar.

  Ismai'il ya shaida wa Manema labarai daga wajen da yake kulle a caji ofis cewa sun yi soyayya da Salamatu har tsawon shekara 8 kuma sun bukaci su yi aure amma lamarin ya gagara.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Saurayi ya kashe budurwarsa domin ta ki ta zubar da cikin shege Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama