• Labaran yau

  Maigida ya gudu ya bar mata domin ta haifi yara 3

  Allah Sarki, wata mata mai suna Mrs. Ugonma Edobor ta shiga matsanancin damuwa tun wata Disamba na bana bayan mijinta ya gudu ya barta har yanzu. Dalilin guduwar mijin shine kawai domin matarshi Ugonna ta haifi jarirai guda uku lokaci daya.

  Majiyarmu ta labarta mana cewa mijin matar mai suna Mr. Pius Edobor wanda ya fito daga kauyen Uromia a jihar ta Edo ya yi batan dabo ne bayan ya killa ido ya ga cewa ai yara uku ne matarsa Ugonna ta haifa masa.

  Yanzu haka an dukufa wajen neman wannan maigida Mr. Pius tare da rokon jama'a ko da Allah zai sa a sami bayanin wajen da yake.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Maigida ya gudu ya bar mata domin ta haifi yara 3 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama