• Labaran yau

  Mahaifi ya gundule kafar wanda ya yi wa diyarsa yar wata 6 fyade

  Wani matashi dan shekara 36 a jihar Edo ya gamu da fushin mahaifin wata jaririya yar wata shida bayan mahaifin jaririyar ya kama matashin yana saka yatsar hannunsa a al'aurar jaririyar sakamakon haka mahaifin jaririyar ya harzuka ya dauko adda ya sare kafar saurayin.

  Rahotonni sun ce yansanda sun kama mahaifin jariyar bisa zargin daukar doka a hannunsa yayin da shi kuma matashin ke fuskantar zargin yin fyade ta hanyar yin amfani da yatsarsa.

  Likitoci sun hada kafar da aka gundule yayin da matashin ke jinya a Asibiti.

   .
  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mahaifi ya gundule kafar wanda ya yi wa diyarsa yar wata 6 fyade Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama