• Labaran yau

  Ka san irin mugun aikin da wannan budurwa ta aikata ? - Hotuna

  Wata budurwa da ke zaune a garin Sapele a jihar Delta ta yi amfani da reza ta yanke saurayinta a wuya  sakamakon wataa gardama da ta sa saurayin ya mare ta ita kuma ta rama ta hanyar yi masa mugun rauni da reza.

  Majiyar mu ta labarta mana cewa lamarin ya faru ne ranar Talata da dare, bayan budurwar ta kai suka tare da bata sunan saurayin ga mahaifiyarshi, cikin fushi shi kuma sai ya mare ta lamari da ya sa ita ma budurwar ta rama ta hanyar yanke shi da reza a wuya.

  Wani matashi ne ya garzaya asibiti da saurayin budurwar inda yanzu haka yake jinya.
   
  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ka san irin mugun aikin da wannan budurwa ta aikata ? - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama