• Labaran yau

  An kashe soji biyu na runduna ta 7 a rikicin kauyen Jos - Hotuna


  Dakarun rundunar soji ta 7 da ke Garrison Jos a jihar Plateau sun kama wasu bindigogi bayan wani tashin hankali da ya auku tsakanin al'ummar Miango da Makiyaya Fulani a kauyen Rafiki ranar Laraba.Jami'an soji biyu ne suka mutu bayan wasu bata gari sun buda masu wata yayin da suka mufato kauyen.

  Jami'an sojin sun gano gawaki 23 a Maraba Dare yar tafiya kadan kafin kauyen Rafiki yayin da aka raunata jama'a da dama.Wasu karin soji guda biyu da suka sami raunuka suna karban magani .

  An kama bindiga kirar AK47 guda daya, harsashi 7.62mm guda 26, karamar bindiga kirar gida da harsashi 15 yayin da dakarun ke ci gaba da sintiri domin tabbatar da tsaro a yankin.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kashe soji biyu na runduna ta 7 a rikicin kauyen Jos - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama