• Labaran yau

  Yadda Gwamna Bagudu ya dira da taimako sakamakon barnar beraye a gonaki

  Manoma a garin Matseri da Gotomo na jihar Kebbi na fuskantar barazanar barnar beraye kan amfanin gonansu na shinkafa. Bayanai sun nuna cewa bayan Magariba ne berayen ke aikata barnar kan amfanin gona na shinkafa. Sakamakon haka ne Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu tare da Mataimakinsa Alh.Samaila Yombe Dabai da sauran manyan jami'an Gwamanati suka ziyarci wasu daga cikin wuraren da lamarin ya shafa a Fadamar Kauyen Gotomo.

  Gwamna Bagudu ya gani da idanunsa irin barnar da berayen ke yi ga gonar shinkafa da Alkama. Ya kuma shaida wa Manoma cewa an bayar da Naira Miliyan 40 domin a sayo maganin beraye a raba wa Manoma a fadin jihar Kebbi. Ya bayyana mamakin ganin cewa har yanzu maganin bai isa hannun Manoma ba kuma ya bayar da umaurni cewa dole ne a gaggauta raba maganin berayen ga Manoma.

  Kai tsaye Gwamna Atiku Bagudu ya ba wani Manomi Abubakar Dodo Ambursa maganin beraye domin ya fara amfani da shi a gonarsa.Haka zalika an ba wani manomi daga garin Indiri maganin .

  Daga bisani Gwamna Bagudu ya taka da kafa a cikin Fadamar har zuwa garin Matseri inda ya zanta da wani Manomi mai suna Abubakar Matseri a gonarsa wanda bera suka taba shukarsa ta Alkama, Gwamna Bagudu ya bashi maganin bera da kanshi tare da bayar da umarni cewa washegari a tabbata an ba kowane Manomi maganin.

  Daga bisani Gwamna Bagudu ya Sallaci Magariba a garin Matseri, kuma ya zanta da jama'ar garin domin sanin matsalolinsu.Daga karshe Gwamna Bagudu ya bayar da kyautar N100.000 domin a tallafa wa Mata da ke cikin gidaje, da N100.000 don Matasan gari sai karin N100.000 domin a ba tsofaffi a garin na Matseri.An mika kudin ne ga Hakimin garin na Matseri.


  Daga Isyaku Garba
  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka
  rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda Gwamna Bagudu ya dira da taimako sakamakon barnar beraye a gonaki Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });