• Labaran yau

  Saurayi ya kashe matashi sakamakon kishi saboda karuwa

  Yansanda a kasar Zimbabwe sun ceci rayuwar wani matashi dan shekara 25 mai suna Tungamirayi Kokerai bayan ya kashe wani matashi ta hanyar caka masa wuka har sau hudu sakamakon kishi akan Karuwa.

  Wata majiya ta labarta cewa a daren Talata ne Tungamirayi Kokerai ya ga wani matashi yana tafiya tare da wata Karuwa da ya dauko ta kwanan gida bayan sun fito daga gidan rawa da misalin karfe 3 na safe a unguwar Phakama.

  Kokerai ya kalubalanci saurayi da ya ga Karuwar tare da shi ya kuma zarge shi cewa yana tafiya tare da budurwarsa lamari da ya kawo zafafar kalamai.

  Daga bisani sai Kokerai ya zaro wuka ya caka wa saurayin har sau hudu, ganin haka ya sa saurayin ya je wani gida kusa da gurin da lamarin ya faru domin neman taimako amma ba'a bude gidan ba. Sai ya jingina a gina daga bisani ya mutu sakamakon zubar jini mai yawa.

  Ganin haka ya sa Karuwa ta tsere yayin da jama'a suka yi wa Tungamirayi Kokerai diran mikiya suka auna masa damen duka kafin yan sanda su zo.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Saurayi ya kashe matashi sakamakon kishi saboda karuwa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });