• Labaran yau

  Mata ta kashe miji bayan ta zuba mashi asid a al'aura don kishi

  Wata mata a birnin Zaria na jihar Kaduna tana rokon hukumomi da yan uwan mijinta su yafe mata bayan mahukunta sun kamata sakamakon zarginta da kashe mijinta saboda kishi.

  Lamarin ya faru ne bayan an tsegunta wa matar cewa mijinta yana soyayya da babbar kawarta har ma ya yi wa kawarta ciki.

  Matar ta gudanar da bincike akan zancen wanda daga bisani ta yi amanna cewa haka zancen yake.

  Sakamakon haka matar ta samo asid a wajen wani mai cajin batur (rewire) mai suna Kabir. Ranar 15 ga watan Fabrairu bayan mijin ta ya dawo daga wajen aiki, matar ta yi kamar bata san da zancen ba kuma bayan ta kawo masa abinci ya gama ci daga bisani da dare ta ja hankalin shi inda suka yi saduwar ma'aurata (jima'i).

  Bayan sun gama saduwa sai miji ya share da barci, ganin haka ke da wuya sai matar da jawo goran asid da ta sayo ta ajiye a karkashin gado sai ta zuba wa mijinta wannan acsd a al'auransa. Sakamakon haka ya sa aka kai mijinta Asibiti mafi kusa inda Asibitin suka ki karban mijin sai suka tura su Asibitin FMC Zaria.

  Rahotanni sun nuna cewa mijin ya rasu ranar Talata 20 ga watan Fabrairu yayin da yake jinya. Sakamakon haka yansanda suka kama matar domin gudanar da bincike.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mata ta kashe miji bayan ta zuba mashi asid a al'aura don kishi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });