• Labaran yau

  Kalli jariri da aka tsinta a unguwar road block a garin Zuru - Hotuna

  An tsinci wani jariri da aka yar a cikin wata laida a unguwar Road Block a garin Zuru na karamar hukumar mulki ta Zuru a cikin jihar Kebbi. Jaririn  dai yana cikin koshin lafiya kuma nan take shugaban karamar hukumar Zuru ya kai dauki inda ya samo mace da za ta shayar da jaririn.

  Rahotanni sun nuna cewa shugaban karamar hukumar Zuru Alh.Muhammed Kabir Abubakar tare da 'yan majalisar sa sun yi namijin kokari domin ceton rayuwar yaron,domin dai bayan samun wacce za ta shayar da shi shugaban ya kuma ba ta taimako na kudi da ababen da suka wajaba domin ta kula da kanta saboda ta sami sukunin shayar da jaririn cikin natsuwa.

  Yanzu dai haka, lamari na jefar da jarirai ya zama ruwan dare kusan a ko ina cikin fadin Najeriya.A watannin baya an tsinci jariri da aka yar a kusa da ofishin JNI a garin Birnin kebbi,haka zalika an tsinci wata jaririya a garin Gwandu sai ga wasu jarirai da aka tsinta shekaran jiya a garin Port Harcourt da wani jariri kuma da aka tsinta a Kaduna da Owerri na jihar Imo.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli jariri da aka tsinta a unguwar road block a garin Zuru - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });