• Labaran yau

  Dogaro da aikin gona shi ne madogaran arzikin talaka -Gwamna Bagudu

  An gudanar da bikin nuna albarkatun gona da tattaunawa akan harkar gona tsakanin manoma da gwamnati a wani shirin hadin guiwa tsakanin jaridar Daily Trust wanda Manir Dan Ali ke shugabanta da Ma'aikatar aikin gona na jihar Kebbi ranar Litinin.

  An gudanar da bikin nuna amfanin gonar ne a harabar Makarantar koyon fasaha na tarayya ta Waziri Umaru da ke garin Birnin kebbi kuma wanda ya sami halarcin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu.

  Gwamana Bagudu ya bayyana muhimmancin dogaro da kai ta hanyar aikin noma tare da yaba wa shugaban kasa bisa bayar da karfi tare da agaza wa sashen aikin gona a Najeriya.

  Haka zalika Manir Dan Ali ya yi magana a kan muhimmancin akin gona ya kuma bukaci jaridu da kafofin watsa labarai su fuskanci yayata lamuran aikin noma domin ta haka za a tallata irin kwazo da manoma ke da shi wanda zai janyo masu saka hannun jari a kan sha'anin noma.

  Daga bisani Gwamna Bagudu tare da Mataimakinsa Col. Samaila Yombe Dabai da manyan baki sun zagaya rumfuna da aka baje kayakin gona.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dogaro da aikin gona shi ne madogaran arzikin talaka -Gwamna Bagudu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });