• Labaran yau

  Dan shekara 40 ya rataye kansa har ya mutu a itaciyar gidansa

  Rahotanni daga jihar Enugu sun nuna cewa wani mutum Kenneth Ugwuattama dan kimanin shekara 40 ya kashe kanshi ta hanyar rataye kanshi a wani itace a harabar gidansa a garin  Iheakpu Obolloafor na karamar hukumar udenu a jihar Enugu.

  Bayanai sun ce an saukar da gawar Kenneth wanda aka gano ranar Laraba bayan makwabta sun gan gawarsa tana lilo a itaciyar harabar gidansa.

  An kai gawar Kenneth a dakin ajiye gawa yayin da hukumomi ke gudanar da bincike akan lamarin.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dan shekara 40 ya rataye kansa har ya mutu a itaciyar gidansa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama