• Labaran yau

  An tsinci gawar mace da ta mutu a cikin rafi

  An tsinci gawar wata mace mai suna Zubaida Nuhu wanda aka tsamo ta a mace daga kogin Tamburawa a jihar Kano ranar Asabar 3 ga watan Fabrairu. Ana zargin cewa Zubaida ta halaka kanta ne ta hanyar fadawa cikin rafin da niyyar kashe kanta.

  Wata majiya ta ce Zubaida ta kammala karatun ta na Degree a Jami'ar ABU da ke Zaria kuma har ta fara Degree na biyu a ABU Zaria. Zubaida ta fara aiki a sashen kula da albarkatun ruwa na Jami'ar kafin aukuwar lamarin.

  Wani mai aikin diban yashi ya shaida wa wani dan jarida cewa Zubaida ta iso kauyen Tamburawa kuma ta tambaya ko wane sashe na rafin ne ya fi zurfi, ya kara da cewa wannan ne lokaci na karshe  da suka gan ta sai daga bisani aka ce an ga gawarta a cikin kogi.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An tsinci gawar mace da ta mutu a cikin rafi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });