• Labaran yau

  An kashe mutane a rikicin kasuwar magani a jihar Kaduna - Hotuna

  Rahotanni daga jihar Kaduna sun nuna cewa an sami tashin hankali da ya yi sanadin mutuwar mutane da ba'a tantance yawansu ba kawo yanzu a Kasuwar Magani a karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna ranar Litinin.

  Wasu hotuna sun bayyana a shafukan yanar  gizo wanda aka ce mutane ne da ake zargin an kashe a rikicin na Kasuwar Magani.

  Gwamna Nasir El-rufai ya bayar da umarni cewa a hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan tashin hankali. Ya kuma yi kira ga jama'a cewa su guji haddasa tashin hankali kuma a zauna lafiya.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kashe mutane a rikicin kasuwar magani a jihar Kaduna - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama