• Labaran yau

  An kama yan fashi 2 bayan motarsu ta yi karo da wata mota - Hotuna

  Jami'an tsaro sun kama wadansu matasa guda biyu da suke kokarin tserewa daga wajen da suka yi fashi da makami a garin Owerri na jihar Imo ranar Talata .An kama matasan ne bayar motar da suke tukawa a guje ta yi karo da wata mota .

  An sami manyan laidodi shake da kudi a cikin motar, bayan matar ta yi karo da wata motar da ke tafe sai daya daga cikin yan fashin ya dauki jakar laida daya makare da kudi ya ruga da gudu.

  Daga bisani jami'an tsaro da suka hada da DSS da yansandan kwantar da tarzoma MOPOL sun dira a gurin kuma suka kama sauran yan fashin tare da sauran kudin suka tafi da su hedikwatar yansanda na jihar Imo.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: An kama yan fashi 2 bayan motarsu ta yi karo da wata mota - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama