YAPA, sabuwar kungiya domin fadakar da matasa kan illolin shaye-shaye a jihar kebbi

Shaye shaye tsakanin matasa a Arewacin Nigeria ya zama ruwan dare kamar yadda kididdiga na hukuma ya nuna, haka zalika masu rike da mukaman zartarwa na gwamnatoci sun koka sakamakon bayanin samun yawan karuwar shaye-shaye a tsakanin matasa.

Bisa wannan dalili aka kafa wata kungiya wadda za ta dinga wayar da kan matasa da al'umma akan harkar sha-shaye, tallace-tallace da kuma illolin zaman banza tare da wayar da kan matasa a kan muhimmancin dogaro da kai ta hanyar koyon sana'oi.

Wannan kungiya ana kiran ta Youth Awareness Progressive Association (YAPA) karkashin shugabancin Mal. Isyaku Garba Chairman na jihar Kebbi, Barr. Sanusi Dan Buga mataimakin Chairman na jiha, Mal. Bello Sidi Sakataren kungiya da sauran mambobin kungiyar.

Manbobin kungiyar sun kai ziyarar ban girma ranar Alhamis ga Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai inda suka jaddada manufar kungiyar wajen kama ma gwamnati wajen fadakar da matasa illolin shaye-shaye tare da neman shawarwari daga Mataimakin gwamna.

A nashi jawabi, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe, ya yaba tare da yin godiya ga tawagar kungiyar bisa manufarsu da suka sa gaba. Yombe ya kuma aminta da mukami da kungiyar ta ba shi na kasancewa Uban kungiyar (grand patron).

Mataimakin Gwamna Alh. Samaila Yombe ya kara da cewa a lokacin da yake aikin soja, ya rubuta littafi akan harkan shaye-shaye a gidan soja, littafin mai suna Drug abuse in Nigeria Army ya ta'allaka ne a kan dalilai,matsaloli da illolin shaye shaye a gidan soja.

Yombe ya yi takaitacce, amma ingantaccen bayani akan harkar shaye shaye, daga bisani kuma ya sanar da 'ya'yan kungiyar cewa suna da jan aiki a gaban su sakamakon wannan manufa ta fadakarwa kan illolin shaye-shaye a tsakanin matasa.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN