• Labaran yau

  Ubandoman Gwandu ya yaba wa Gov. Bagudu yayin tarbon kungiyar YAPA na jihar Kebbi

  Uban doman Gwandu Alh. Halidu Sa'ad ya yaba wa mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu bisa namiji kokari da ya yi wajen sama wa matasa aikin yi musamman ta bangaren aikin noma a fadin jihar Kebbi. Basaraken ya ce wannan Gwamnati karkashin Gwamna Atiku Bagudu ta zama zakara daga cikin Gwamnatoci da suka gabata domin ita ce ta wadatar da matasa da aikin yi ta fannen noma da ya kai ga nassarori da aka samu wajen bunkasar kayan abinci a fadin jiha.

  Ya yi wannan jawabi ne yayin da ya karbi bakoncin tawagar kungiyar Youth Awareness Progressive Association (YAPA) na jihar Kebbi a gidansa da ke 'Yar yara a garin Birnin kebbi.Basaraken ya bayyana wa wakilan kungiyar yadda karkashin Gwamna Bagudu da Mai Martaba Sarkin Gwandu suka dukufa wajen inganta tsaro a jihar Kebbi tare da hadin gwuiwa da jami'an tsaro na jiha.

  Shugaban kungiyar ta jihar Kebbi Mal. Isyaku Garba ya shaida wa basaraken cewa sun ziyarce shi ne domin su shaida masa manufofin kungiyar tare da tsarin irin ayyuka da ta kuduri aiwatarwa. Haka zalika Mal. Isyaku Garba ya ce kungiyar tana da wakilci a kananan hukumomi na jihar Kebbi ya kuma yi godiya ga Ubandoma bisa kyakkyawar tarbo da aka yi masu.

  Tawagar shugabannin kungiyar sun kunshi Mal Isyaku Garba shugaban kungiyar na jihar Kebbi,Barr. Sanusi Danbuga Argungu mataimakin shugaba, Bello Sidi Birnin kebbi Sakatare, Nasiru Sani Ma'ajin kungiya, Abu Sufiyanu PRO1, Hashimu Arzika Gudi PRO2, Alh Dahiru Umra, Alh. Buhari Sauwa da sauran 'ya'yan kungiyar.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Ubandoman Gwandu ya yaba wa Gov. Bagudu yayin tarbon kungiyar YAPA na jihar Kebbi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama