• Labaran yau


  Shugaba Buhari da Obasanjo sun hadu bayan cecekucen wasiku

  Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo a birnin Addis Ababa yayin da ake bude babban taron Kungiyar Afirka, wato AU na 2018.

  Shugabannin sun gaisa kuma sun yi magana da juna na kimanin minti biyu.Tsohon shugaban kasa Abdussalami Abubakar, wanda shi ma yana halartar taron ya dauki hoto tare da shugabannnin biyu.

  A makon jiya ne tsohon shugaban kasa Obasanjo ya rubuta wata wasikar wadda a cikinta yake kira ga shugaba Buhari da kada ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019.Obasanjon ya kuma tuhumi Buhari da kasa farfado da tattalin arzikin kasar, da kuma nuna fifiko ga wasu na kusa da shi.


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

  Daga BBC
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Shugaba Buhari da Obasanjo sun hadu bayan cecekucen wasiku Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama