Mutum 8 sun mutu sakamakon konewar mota a karamar hukumar Shanga (Hotuna)

Daga Sani Musa Saminaka da Isyaku Garba |
 
An sami aukuwan wani ibtila'i sakamakon konewar wata motar bus wanda ya yi sanadin mutuwar mutum takwas a ciki.Hatsarin ya faru ne tsakanin tashar rogo zuwa Girommasa a cikin karamar hukumar mulki ta Shanga.

Wakilinmu ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan wasu daga cikin fasinja da ke cikin motar suka ankara cewa akwai alamun cewa motar za ta iya kamawa da wuta.

Sakamakon haka direban ya tsaya nan take, kuma tsayawarsa ke da wuya sai motar ta kama da wuta tare da fasinja a ciki wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutum takwas bayan sun kone gaba daya.

Amma mutum biyar sun tsira har da direban motar wasu fasinja kuma an garzaya da su zuwa Asibiti domin samun kulawa.

Wakilinmu Sani Musa Saminaka ya zanta da direban inda ya shaida masa cewa sunansa Umaru Giredi Argungu, ya kuma shaida ma wakilin namu cewa motar ta taso ne daga Lagos zuwa garin Silame a jihar Sokoto kafin aukuwar lamarin ,ya kara da cewa mutum 18 ne ke cikin motar

Umaru ya ce ya shafe shekara 20 yana tuka motar jigila amma sai wannan lokaci ne Allah ya jarrebe shi da wannan hatsari na konewar mota tare da mutane a ciki. Ya kara da cewa dama tun da safiyar yau ya yi arangama da yan fashi a hanya Allah ya kubutar da shi , sai ga wannan jarabawar kuma.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN