• Labaran yau


  Ma'aikacin Majalisa ya rama mari da wata Sanata ta sa aka yi masa

  Wata takaddama ta taso tsakanin wata Sanata mai suna Biodun Olujimi bayan an zarge ta cewa ta ba wani mai taimaka mata umurni cewa ya mari wani ma'aikacin Majalisa kawai domin ya shiga na'urar zirga-zirga na Elevator ko Lifter tare da ita wanda nan take ma'aikacin Majalisar ya rama ta hanyar waska wa Sanatar mari marmakin mai taimaka mata da ta sa ya mare shi ranar Litinin.

  Bayanai sun nuna cewa Ma'aikacin da aka mara dan kungiyar ma'aikatan Majalisai na Najeriya ne ta PASAN. Wannan lamari ya jawo ala tilas jami'an tsaro na Majalisa suka shiga tsakani.

  Sauran ma'aikatan Majalisar sun ki bayar da sunan ma'aikacin da lamarin ya faru da shi .

  Sanatan ta sha alwashin ganin cewa an hukunta ma'aikacin Majalisar


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ma'aikacin Majalisa ya rama mari da wata Sanata ta sa aka yi masa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama