• Labaran yau

  Labarai a yau Talata 2/1/2018

  Shekara ta 2017 ta wuce ,yayin da aka shiga sabuwar shekara 2018 ranar Litinin da ta gabata.Haka zalika shekarar 2017 ta wuce da wasu fitattun 'yan Najeriya
  Karanta nan don sanin fitattun 'yan Najeriya da suka mutu a 2017.

  Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa al’ummar kasar jawabi na sabuwar shekara inda ya bayyana ayyukan dogo da hanyoyi da kuma wutar lantarki da gwamnatinsa za ta gudanar a shekarar 2018.
  Daga cikin manyan ayyukan da za a gudanar a wannan shekarar, akwai titin jirgin kasa (dogo) da zai kama daga Kano ya ratsa da Kazaure da Katsina har zuwa Maradi na Jamhuriyar Nijar. Da kuma titin hanyar Abuja zuwa Kaduna har zuwa Kano

  Shugaban Cocin Latter Rain Assembly da ke Jihar Legas, Pastor Tunde Bakare ya ce Ubangiji ne Ya sanar dashi cewa ya nemi Shugaban Kasa.
  Tuned Bakare ya sanar da hakan ne a lokacin taron ibadar sabuwar shekara day a gudana a Cocinsa.  


  “Da misalin karfe hudu na safiyar Lahadi. Sai Ubangiji Ya ce mani ‘kada ka yi watsi da harkar siyasa, akwai sauran abun da ake bukata daga kai. Ka nemi Shugaban Kasa’. Don haka zan nema idan lokaci ya yi,” in ji Pastor Bakare.
  Pastor Bakare ya kara da cewa, “Na so in bar wa kaina wannan maganar ba tare da sanar da kowa ba saboda wasu za su yi murna, wasu kuma za su Allah wadai. Amma ruhi mai tsarki ba zai bari in yi shiru ba.”

  Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fito a wani faifan bidiyo inda ya ce kungiyarsa ce ta kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya.

  Bidiyon mai tsawon minti 31 da dakika 53 ya nuna shugaban Boko Haram din sanye da farar riga tare da bindiga a jingine a kafadarsa.

  Shekau dai ya yi magana ne cikin harshen Larabci da Hausa kuma ya karanta da yawa daga cikin maganar da ya yi da harshen Larabci ne daga cikin wata takarda rike a hannunsa. Karanta saura >>>


  Babban Limamin Cocin, ‘Christ for All Peoples,’ da ke Ojoo, a Jihar Lagos, Prophet Samuel Oyadara, ya kirayi Tsohon Shugaban kasarnan, Cif Olusegun Obasanjo, da ya tuba ya kuma roki Allah gafara a kan zunuban da ya aikata, tun kafin ya Mutu. Sannan kuma ya kirayi Jagoran Jam’iyyar APC,na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya dukufa da addu’a a kan masu nufin su yi masa kisan gilla a cikin wannan shekara ta 2018.

  Read More at: https://hausa.leadership.ng/2018/01/01/fasto-ga-obasanjo-ka-tuba-kafin-ka-mutu/
  Babban Limamin Cocin, ‘Christ for All Peoples,’ da ke Ojoo, a Jihar Lagos, Prophet Samuel Oyadara, ya kirayi Tsohon Shugaban kasarnan, Cif Olusegun Obasanjo, da ya tuba ya kuma roki Allah gafara a kan zunuban da ya aikata, tun kafin ya Mutu. Sannan kuma ya kirayi Jagoran Jam’iyyar APC,na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya dukufa da addu’a a kan masu nufin su yi masa kisan gilla a cikin wannan shekara ta 2018.

  Read More at: https://hausa.leadership.ng/2018/01/01/fasto-ga-obasanjo-ka-tuba-kafin-ka-m


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Labarai a yau Talata 2/1/2018 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });