Kungiyar YCMA ta fara aiki don ci gaban kasar Yauri

Wannan wata kungiyace mai fafutakar bada gudummuwa ga al'ummar kasar Yauri bakidaya da karfinsu.

Ita dai wannan kungiya tana gudana ne akarkashi jagorancin wa'yansu mutane kamar haka :
Com.Umar Tukur Geography (Chairman)

Zayyanu Abubakar (V.C)

Com. Ahmad Dudu (Secretary G) da kuma Saminu Musa (ma'aji).

Ganin yadda wannan kungiyar ke bada jininta tukuru wurin yiwa mutane aiki batareda Neman wani abu nasuba , yasa naga shugaban wannan tafiya (Geogrphy) na kuma tattauna dashi kamar haka:
Tambaya:

Mal.Tukur naga kuna ta aikace-aikace wurare daban-daban kamar nan cikin garin Yauri kunyi gyare-gyare a babbar Asibitin gwamnati , kuma kunyi irin wannan aiki amakarantar Mata(GGSC) , kuma kun ziyarci Wara da irin wannan aikin , kun kuma ziyarci karamar hukumar Shanga da irin wannan aikin , uwa-ubama naga wannan hanya ta Yauri wadda kusan kowane Direba yana hasale da ita , har itama naga kuna gyara , shin gwamnatice ta saku wannan aikin ko wata kwangilace kuka karbo  a wani wuri ?

Ams: 

Alhamdulillahi naji dadin wa'ynnan tambayoyin da kayi.

Farko dai ina son ka sani babu wani sisin kwabo da ake bamu a gwamnatance akan wannan aikinnamu. Hasalima da kudimmu muke aikace-aikacemmu amma kuma alhamdulillahi wasu jama'a suna bada nasu gudummuwa sosai ganin yadda muke aikin batareda cilaswa kawaba.

Tamb:

Wannan kungiyar ta Dade da kafawa ?

Ams: 

Yau kusan wata biyar kenan da assasa wannan kungiyar.

Tamb:

To menene babban maksudin ta , domin naga akwai wasu kungiyoyi da yawa a wannan masarautar ta Yauri ?

Ams:

Tabbas akwai kungiyoyi da yawa kamar yadda kace amma munyi l'akarine da bukatarda jama'a suke dane a gwamnantace , shine sai muka zabi mu fara rage wasu kamin gwamnatin ta zo da nata, musamman kan wa'yannan abubuwa da mukeyi.

Shi yasa muka yi dogon nazari daga baya muka ya dace muhada wannan kungiyar kuma cikin ikon Allah ta samu karbuwa fiyeda yadda muka zata.

Babbar manufar itace, bada gudummuwa ga jama'ar wanna yankin namu daidai da bukatarsu.
Tamb: 

To yanzu kuna da wani guri na fitarda 'yan siyasa daga cikinku ko kuwa ?
Ams;

A'a ahalin yanzu bamuda wannan gurin , karshema muna iya kokarin mu na ganin cewa mun kaucew rigimar siyasa domin kada tayi muna illa acikin wannan tafiya.

Tamb:

Ko akwai wasu dattawa da suka tofa albarkacimbakin su akan wannan tafiya taku ?
Ams:

Kwarai kuwa mai-martaba Sarkin Yauri (Dr.Muhammad Zayyanu Abdullahi) ya sa muna albarka ya kuma yi muna tsokaci sosai tareda janhankalimmu amatsayin sa na Uba garemu.
Tamb:

Na samu labarin cewa kunje birnin kebbi jiya , me ya kaiku tunda kace bakuda alaka da siyasa a wannan tafiyar taku ?

Ams:

Kwarai kuwa , munje domin haduwa YAWURAWA ma zauna birnin susanda zamanmu domin Idan bukatarsu ta taso to za'a nemesu domin ahadu araya kasar baki daya, wannan shi ya kaimu bawai munje wurin wani Dan siyasa bane kamar yadda mutane ke zato.

To madalla.

Com.Umar Tukur mun gode sai ka sake jimmu nan gaba kadan.

Daga Sani Musa Saminaka

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN