• Labaran yau

  Gwamnan jihar Niger ya ceci wasu dalibai daga hannun bata gari - Hotuna

  Gwamnan jihar Niger Abubakar Sani Bello ya ceci wasu samari guda biyu bayan wasu matasa sun yi masu dukan tsiya yayin da suke dawowa daga makarantar gwamnati na jeka ka dawo a garin Minna. samarin guda biyu sun sami raunuka da ya haifar da zubar jini kafin isowar Gwamnan a wajen da lamarin ya faru a gaban Makarantar koyon ilimi da ke Minna.

  Gwamnan yana kan hanyarsa ce ta zuwa Tungar Malam a karamar hukumar Paiko tare da tawagarsa yayin da ya hango taron jama'a sakamakon lamarin kuma nan take Gwamnan ya bayar da umaurni a tsaya yanayi da ya sa matasan suka ranta na kare.Wata majiya ta ce matasan sun fito ne taga unguwa makwabta na Sango da ke a birnin Minna.

  Ganin lamarin da ya faru sai Gwamnan ya bukaci Likitansa Dr. Shehu ya duba su kafin motar daukan marasa lafiya na tawagar Gwamnan ta zo ta dauke su zuwa Asibitin kwararru na IBB da ke garin Minna.

  Daga karshe Gwamnan ya bukaci kwamishinan yansanda na jihar Mr Paul Yakadi cewa a zakulo wadanda suka aikata wannan aikin domin a hukunta su.
   

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gwamnan jihar Niger ya ceci wasu dalibai daga hannun bata gari - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });