• Labaran yau

  Gobara ta yi sanadin mutuwar yara hudu a Zamfara

  Ma'aikatan kashe gobara ta jihar Zamfara ta ce yara hudu ne suka rasa ransu a wata gobara da ta auku a gidan wani direba wanda yake aiki a gidan gwamnatin jihar Zamfara. Gobarar ta auku ne a unguwar Awala Filin Jirgi a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

  Yaran da suka mutu a gabarar maza biyu ne da mata biyu a daren ranar Talata da misalin karfe 10 na dare.

  Shugaban ma'aikatan kashe gobara na jihar Zamfara Mr. Jibo ya ce sun sami kiran ko ta kwana da misalin karfe 10 na daren Talata , amma kafin su isa wurin gobarar ta riga ta ci karfin ginin. Ya kara da cewa sun yi amfani da tanka hudu domin kashe gobarar.

  Mr. Jibo ya yi kira ga jama'a cewa su dinga bin ka'idodi domin kiyaye hadarin tashin gobara, ya kara da cewa alamu sun nuna cewa gobarar ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gobara ta yi sanadin mutuwar yara hudu a Zamfara Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });