• Labaran yau


  Gobara ta kone kasuwar garin Dabai a karamar hukumar Zuru

  Da misalin karfe 10:00 na safen ranar Juma'a gobara ta tashi a kasuwar garin Dabai a karamar hukumar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi. Ba a san musabbabin tashin gobarar ba kuma kawo yanzu ba'a kammala hada kiyasin adadin barnar da gobarar ta yi ba.

  Amma wata majiya ta shaida mana cewa ana zargin cewa tashin wutar zai iya kasancewa sakamakon harkar 'yan shaye shaye wadanda suka jefar da konon sigari kasancewa lokacin hunturu ne da iska ke kadawa.

  Bayanai sun nuna cewa mahunkunta a karamar hukumar ta Zuru sun shaida wa hukumar agaji na gaggawa a jihar Kebbi watau SEMA inda ake hada bayanai domin turawa ga hukumar a garin Birnin kebbi.

  Shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru Alh. Muhammed Kabir Abubakar ya shaida mana cewa majalisar sa ta tsara wani shiri domin ganin cewa an ci kasuwa mai zuwa a kasuwar daidai karfin karamar hukuma kafin samun agaji daga hukumar SEMA ya iso.

  Hawansa mulkin karamar hukumar mulki ta Zuru, shugaban karamar hukumar Alh. Muhammed Kabir Abubakar ya gyara motar kashe gobara da ta dade a lalace, sakamakon haka motar ta taka rawa wajen kashe gobarar ta kasuwar ta Dabai tare da taimakon mazauna unguwar.

  Alh. Muhaammed Kabir ya ce majalisarsa ta dauki wasu matakai na tsaro domin ganin cewa irin haka bai sake aukuwa ba.

  Wadanda suka isa wajen a mataki na gaggawa sun hada da Shugaban karamar hukumar Zuru Alh. Muhammed Kabir Abubakar, Sarkin Dabai Muhmmed Shehu Rikoto, Daniel Wase chiyaman mazabar Dabai, Kansilan Dabai, Kansilan Rumu Daben Seme,Sakataren Masarautar Dabai da kuma jama'ar kasar Dabai

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gobara ta kone kasuwar garin Dabai a karamar hukumar Zuru Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama